Podchaser Logo
Home
Dandalin Fasahar Fina-finai

France Médias Monde

Dandalin Fasahar Fina-finai

A daily News and Politics podcast
Good podcast? Give it some love!
Dandalin Fasahar Fina-finai

France Médias Monde

Dandalin Fasahar Fina-finai

Episodes
Dandalin Fasahar Fina-finai

France Médias Monde

Dandalin Fasahar Fina-finai

A daily News and Politics podcast
Good podcast? Give it some love!
Rate Podcast

Episodes of Dandalin Fasahar Fina-finai

Mark All
Search Episodes...
Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi  bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.
A cikin wannan shirin na dandalin fasahar Fina-finai,Hawa Kabir ta samun tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar fina-finai dangane da makomar mata musaman a gidajen mazan su,ko wandada ke da niyar yin aure.
Kamar yadda aka saba kowane mako shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai tare da Hauwa Kabeer ya tattauna akan wasu daga cikin muhimman al'amuran da ke wakana a masana'antar fina-fina da ke arewaci da kuma kudancin Najeriya.
Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer, ya leka kungiyar MOPAN ne domin jin wainar da ake toyawa.
A cikin shirin duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harakar fim yan lokuta bayan kamala zaben wakilan MOPAN a jihar Kaduna.Makomar duniyar Fim,hanyoyin kawo karshen baraka a wannan duniya na daga cikin manyan
Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da wani fitaccen mawakin Hausa da ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i.
Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai ya leka inda ake daukar shirin barkwancin nan mai dogon zango, wato 'Gidan Badamasi', inda ya gana da jarumai da masu ruwa da tsaki a shirin, cikin su har da babban daraktan shirin, Falalu Dorayi.
Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya.Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu ab
Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir ya tattauna na masu ruwa da tsaki kan rubutun adabin Hausa da kuma fina finai kan rasuwar marigayi Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi.
Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai tare da Hauwa Kabir ya cigaba da tattaunawa ne kan taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC da ya gudana a garin Zaria, dake jihar Kaduna.
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai, hauwa Kabir ta leka taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC  da ya gudana a Zaria, jihar Kaduna. Shirin ya gana da shehunan malaman da suka halarci taron. 
A cikin shirin dandalin Fina-finai,Hawa Kabir ta jiyo ta bakin  masu shirya fim a Nollywood,wanda suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su da kuma irin wasannin da suke iya kasancewa a cikin su ga baki daya.
Shirin dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan rashin da masana'antar Kannywood tayi na wasu manyan jaruman ta, musamman Ahmad Aliyu Tage da ya rasu a makon da ya gabata.
Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako tare da Hauwa Kabir ya kawo mana ta'aziyyar mawakin siyasan nan, Isyaku Forest, wanda ya rasu kwanan nan. Hauwa Kabir ta tattauna da makusanta da aminansa, ciki har da shahararren mawakin siya
Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan dalilan da suka janyo faduwar kasuwa fina-finan Hausa.
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa kabir ta kawo abubuwa da dama a bangaren fina-finai, inda ta duba yadda yanzu masana'antar Kannywood ke gogayya da takwararta tav kudancin Najeriya. Ta kuma tattauna da shugaban jaruman Kannywo
Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da Muhammadu Nura Yakubu da a yanzu aka fi sani da sunan Yaya Dankwambo na shirin fim din Gidan Badamasi.
Shirin Dandalin Fasahar Fina Finai ya tattauna da Tijjani Asase da aka fi sani da Damisa kan lamurran da suka shafi masana'antar Kannywood.
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta duba tattauna da Ado Ahmed Gidan Dabino a game da ci gaban shirin fim din Malam Zalimu. Bayan nan ta leka Nollywood ta kudancin Najeriya, inda ta kawo ta'aziyar rasuwar shahararren maw
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta yi dubi da batun kasuwanci a masana'antar Kannywood, tare da duba yadda masu shirya fim din suka koma intanet, ta wajen cin moriyar dandalin Youtube, inda suke dora ayyukansu a kai.
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon, Hauwa Kabir ta kawo ta'aziyyar jarumar Kannywood da Allah ya wa rasuwa a makon da ya gabata,inda ta tattauna da abokan aikinta na Kannywood. Shirin ya kuma leka Nollywood da Bollywoo
Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan yadda Jarumai musamman mata a musamman a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood ke fuskantar cin zarafi daga masu kallo a kafafen sada zumunta na zamani.
Mawaka fina-finai a Najeriya na rayuwa ba tareda sun ci moriyar aikin da suke yi ba,banda haka Hawa ta samu tattaunawa da Haro mawakin hausa a Kaduna dake Najeriya.A cikin shirin Duniyar Fina-finai tareda Hawa Kabir,ta samu tattaunwa da wasu da
Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir, ya tattauna da wasu tsoffin 'yan wasan Kannywood cikinsu har da Isa Bello Ja. Kana shirin ya kuma tattaunawa dangane da cacar baki da fitattun mawakan Kudancin Najeriya mat
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon, Hauwa Kabir ta tattauna da wasu fitattun jaruman Kannywood, ta kuma leka Nollywood, na kudancin Najeriya don ganin wainar da ake toyawa.
Rate

Join Podchaser to...

  • Rate podcasts and episodes
  • Follow podcasts and creators
  • Create podcast and episode lists
  • & much more

Unlock more with Podchaser Pro

  • Audience Insights
  • Contact Information
  • Demographics
  • Charts
  • Sponsor History
  • and More!
Pro Features